Daga Ibrahim Muhammad Kano
Gwamnan jihar Kano.Abba Kabir Yusuf ya bayyana Dangote a matsayin hazikine da ayyukan taimakonsa ke tallafawa bunkasa rayuwar miliyoyin yan Najeriya da ma nahiyar Afirka baki daya.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban daraktan sa na yada labarai da yada labarai Sanusi Dawakin-Tofa ya fitar na taya Alhaji Aliko Dangote murnar cika Shekaru 67 a Duniya.
Ya ce Dangote ya kasance babban kashin baya ga tattalin arzikin kasa kuma yana da matukar muhimmanci ga ci gaban Afirka.
Ya ce Jihar Kano da take mahaifar Dangote al’ummar ta na godiya bisa karamci na jin kai da yake. musamman rabon kayan jin kai ga miliyoyin marasa galihu da tallafawa manufofin Gwamnatin Jihar Kano da hakan zai haifar da ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.
Abba Kabir Yusuf ya yi fata da addu’ar tsawon rai da lafiya da bunkasar cigaban arziki ga shugaban rukunin na kamfanonin Dangote.Alhaji Aliko Dangote.