Kungiyar Wakilan Jaridu Reshen Jihar Kano Ta Yi Alhinin Rasuwar Wakilin Jaridar Leadership

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Ibrahim Muhammad kano

Kungiyar wakilan jaridu ta Najeriya NUJ, ” Correspondents Chapel ta kasa reshen jihar Kano ta bayyana alhinin ta game da rasuwar mambanta Abdullahi Yakubu, wakilin jaridar LEADERSHIP a jihar Kano.

Marigayi Yakubu ya rasu ne a ranar Juma’a yana da shekaru 55.Gogaggen dan jarida, Marigayi Yakubu ya fara aikin jarida ne da jaridar Triumph dake Kano.

Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Kano, Alhaji Aminu Garko, a cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai ya bayyana marigayi Yakubu a matsayin gogaggen dan jarida kuma hamshakin mutum wanda ya rasu a daidai lokacin da ake bukatar hidimarsa ga bil’adama.

Aminu Garko yace Malam.Abdullahi Mutum mai saukin kai, ya yi aiki a Sakkwato a matsayin wakilin Jaridun Triumph na jihar.

Ya kasance Shugaban kungiyar ‘Yan jarida reshen Jihar Jigawa lokacin da ya yi aiki a matsayin wakilin Jaridun THISDAY kafin ya shiga jaridun LEADERSHIP, sannan ya koma Kano.

Kyakkyawan gudummawar da ya bayar ga aikin jarida ba za ta kasance ba za ta gushe ba a cikin zukatan al’umma.Mutum ne kishin addini.

Malam.Abdullahi Yakub ya rasu ya bar mata da ’ya’ya da dama kuma t an binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

“Muna rokon Allah ya gafarta masa ya, kuma ya ba shi Janatul Furdausi, Amin.”…..inji Aminu Garko.

Share.

About Author

Comments are closed.