Kotu Ta Kori Karar Peter Obi Kan Nasarar Zaben Tinubu

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kotun daukaka karar zaben shugaban kasa ta kori karar Peter Obi na Jam’iyyar Obi ya shigar na neman soke nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa bisa zargin, rashawa fataucin miyagun kwayoyi da kuma rashin takardun shaidar kammala karatu.
Alkalan kotun sun kuma yi ittifakin cewa Obi da jam’iyyarsa sun gaza tabbatar da ikirarinsu cewa shi ne ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, ba Bola Tinubu na Jam’iyyar APC ba.
Sun kuma gaza tabbatar da laifukan da suke zargin Tinubu ballantana samun sa laifi, kamar yadda suka yi ikirarin wata kotu a kasar Amurka ta yi.
Hasali ma, tun a shekarar 2003, gwamnatin Amurka ta hannun ofishinta na jakadanci a Najeriya ya sanar da Shugaban ’Yan Sandan Najeriya cewa gwamnatin kasarsa ba ta da wani bayani game da manyan laifukan da ake tuhumar ba.
Zargin safarar haramtattun kudade kuma ba babban laifi ba ne a Amurka, sabanin matsayinsa a dokar Najeriya.
Kotun ta kuma yi fatali da zargin Obi na rashin halascin takarar Tinubu a zaben kan zargin fataucin miyagun kwayoyi da rashin takardun shaidar kammala karatu.
Ta kuma yi watsi da 10 daga cikin shaidu 13 da LP ta gabatar, bisa hujjar cewa wa’adin da doka ya tanada na ba da shaida ya wuce kafin su ba da shaidarsu.
Alkalin da ya karanta hukuncin, Abba Bello Mohammed, ya bayyana cewa masu karar sun kasa tabbatar da zargin da suke yi da kuma ikirarinsu na cewa Obi ne ya samu kuri’u mafiya yawa kuma za su gabatar da sahihin sakamakon zaben.
Peter Obi da jami’yyar sun daukaka kara ne suna ikirarin shi ne ya samu kuri’u mafiya yawa a zaben, amma aka murde, aka yi wa Tinubu kari.
Sun kuma yi ikirarin tauye yawan kuri’un da aka samu, tare da sanar alkaluman bogi, tare da cewa suna da sahihan alkaluman.
Sauran ikirarin sun hada da barazana ga magoya bayansu da kuma saba tanade-tanaden dokar zabe, wadanda a bisa su ne suke kira ga kotun ta soke zaben Tinubu, ta ayyana Peter Obi a matsayin zababben shugaban kasa.
Amma alkalin ya ce jami’yyar ta kasa tabbatar da cewa dan takararta ne ya samu kuri’u mafi rinjaye, haka kuma sun kasa tabbatar da wuraren da suka ce an yi aringizo, sannan sun kasa kawo sahihin sakamakon zaben da suka yi ikirarin suna da shi.
Masu karar sun kuma kara tabbatar da ikirarinsu na cewa kuri’un da aka kada a wasu rumfunan zabe sun zarce yawan masu zabe a rumfunan.
Haka kuma jam’iyyar ta rika yin kudin goro game da zargin rashawa da barazana a jihohin Ribas, Benue, Legas, Taraba, Imo da Osun amma ta kasa ayyana wuraren da haka ya faru.

 

Share.

About Author

Comments are closed.