APC Ta Kara Dakatar Da Mambobinta 26 Kan Zargin Zagonasa A Jihar Osun

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Biyo bayan korar da Jami’yyar APC reshen jihar in Osun ta yiwa wasu ‘ya’yanta guda 84 a ranar Larabar da ta wuce, kan zargin yiwa jam’iyyar zagon kasa, ta kuma kara sanar da dakatar da karin wasu ‘ya’yanta guda 26 bisa zafin su da yiwa jam’iyyar zagon kasa.

APC a jiya Alhamis ne ta sanar da dakatar da su a cikin wata sanarwa da shugaban ta jihar Mista Sooko Lawal ya fitar.

Lawal ya ce, an dakatar da su ne saboda korefe-korafen da zargin raba kan jam’iyyar da wasu ‘ya’yan APC suka yi akansu.

Ya ci gaba da cewa, biyo bayan korefe-korafen na yin zagon kasan ne, babban kwamitin APC na jihar ya kafa kwamitin ladartabtar wa domin gudanar da bincike kan zargin da ake yi masu.

A cewarsa, bayan kwamitin ya yi nazari kan zargin babban kwamitin APC na jihar bayan ya tattauna akan sakamakon binciken kwamtin na ladarbtar wa tare da yin dubi akan hujjojin ya yanke shawarar dakatar da su.

Wadanda dakatarwar ta shafa su ne, Alhaji Moshood Adeoti, Najeem Salami, Sanata Mudasiru Hussain, Adelowo Adebiyi, Mista Adelani Baderinwa, Mista Sikiru Ayedun, Kazeem Salami, Alhaji Adesiji Azeez, Gbenga Akano.

Sauran sun hada da, Mista Kunle Ige, Mista Biodun Agboola, Gbenga Awosode, Rasheed Opatola, Gbenga Ogunkanmi, Israel Oyekunle, MBO Ibraheem, Akeem Olaoye, Francis Famurewa, Mista Tajudeen Famuyide.

Kazalika akwai kuma iwargida Adenike Abioye, Wasiu Adebayo, Rasheed Afolabi, Mista Segun Olanibi, Mista Tunde Ajilore, Mista Ganiyu Ismaila Opeyemi, Zakariah Khalid-Olaoluwa.

Share.

About Author

Comments are closed.