Ambaliyar Ruwa Ta Raba Mutum 563 Da Muhallinsu A Jihar Adamawa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Ambaliyar ruwan sama ta raba mutane 563 da ke a Unguwan Tana a karamar hukumar Yola ta gabas a jihar Adamawa.

Mutanen da iftila’in ya shafa, a yanzu haka sun samu mafaka a makarantar sakandare ta jeka ka dawo GDS da ke yankin Limawa-Jimeta, a Yola babban birnin jihar.

Shugaban makarantar Musa Hassan Jada ya bayyana cewa, mutanen da abin ya shafa sun tare a Ajujuwan bakwai da makarantar take da su.

Kazalika, mataimakin gwamnan jihar Kaletapwa George Farauta, ziyarci Unguwan Tana domin duba irin barnar da ambaliyar ruwan ta janyo.

Bugu da kari, George ya yi alkawari gwamnatin jihar, za ta kawo masu dauki domin a rage masu radadin zafin aukuwar iftila’in na ambaliyar ruwan.

Amabilayar ruwan dai ta auku ne sanadiyyar cikar da kogin Benuwe ya yi biyo bayan yin ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da kuma sako ruwan Dam na Lagdo da ke a jamhiriyar Kamaru.

Share.

About Author

Comments are closed.