“Hukuncin Kotun Koli Kan Bai Wa Kananan Hukumomi Kudadensu Kaitsaye Zai Bunkasa Ci Gaban Al’umma”

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Malam Abdul’azeez Abdul’azeez mataimaki na musamman ga shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu akan yada labarai ya bayyana cewa kara da Gwamnatin tarayya ta kai kan takaddamar kudaden karanan hukumomi ba domin cin zarafi ko nuna ya tsa ga Gwamnoni ba ne anyi ne don ganin domin warware matsalar da yan kasa suka jima suna kokawa akan yanda aka danne tsarin kananan hukumomi.

Ya yi nuni da cewa Ita dama kotun koli ita ce take da alhakin yin fassarar tsarin Mulkin Nijeriya idan akwai wata takaddama ko rashin fahimta ita ta yanke hukuncin na karshe.

Abdul’azeez Abdul’azeez ya kara da cewa ada sun sani tsarin cin gashin Kananan hukumomi yana da matukar tasiri da amfani da taimakawa wajen samar da tsaro da abubuwan bunkasa rayuwa na yau da kullum da shigar da kuɗade hannun jama’a a birni da karkara.

Ya ce za a sami cigaba.a birni da karkara da dama kamar yin hanyoyi tsakanin wannan kauye zuwa wannan da gina kasuwa da kulada lafiya a Matakin farko.Don haka hukuncin da kotun koli ta zo dashi ta nuna rashin daidai wajen rike dukiyar kananan hukumomi domin ba a yi ta domin Gwamnoni su zasu juyata ko sarrafa yanda zata kashe kudi ba.

Ya ce wannan ta saka kotu ta ce a rika turawa Kananan hukumomi kudinsu kai tsaye ko a 1999 zuwa 2007 Kananan hukumomi na cikin walwalla har tallafin karatu da sauran abubuwa na yau da kullum suke gudanarwa amma yanzu irin wadannan abubuwa sun tsaya.

Muna fata Gwamnoni idan sun tsaya sun bi dokar yanda take Basu biyo wata hanya ta yiwa hukuncin katsalandan ko manakisa gareshi ba za a sami cigaba kwarai da gaske zai kawo cigaba wajen inganta tsaro da samarwa talaka sauki.

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa akan yanda labarai ya ce burin shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu shine a samarwa talaka sauki a samar da hanyoyi da zasu kawo rangwame kuma a matsayinsa wanda ya yarda da tsarin Damakwaradiyya da tsarin mulki shine abi abinda doka tace ba cuta babu cutarwa shine makasudin zuwa kotun koli kuma ya yi farin ciki sosai da hukuncinda ta yi.

Share.

About Author

Comments are closed.