Daga Ibrahim Muhammad Kano
A ci gaba da ayyukan jinkan al’umma da Gidauniyar ta Ta Malam ta saba gudanarwa a fannoni daban-daban karkashin jagorancin Dakta Saleh Musa Wailare ta rabawa manoma ta kaiwa manoma a Kananan hukumomin Danbatta da makoda dauki na basu tallafin taki.
Wannan tallafin na zuwa ne a daidai wannan lokaci na Damina da manoma ke mutukar bukatar takin amma Sakamakon tsada da ya yi yawanci manoman sayen takin ya gagaresu.
Dakta Saleh Musa Wailare ya raba takin zamanil na ruwa guda 500 ne kyauta ga manoman na Kananan hukumomin Danbatta da makoda a ranar Asabar da hakan ya yi mutukar sanya farin ciki ga dibin manoma da suka amfana.
Baya ga wannan jagoran na Gidauniyar na Ta Malam Dakta Salen Musa Wailare kamar yanda ya saba ya samawa Matasa guda 10 aikin tsaro a Gwamnatin tarayya.